1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Irak ta gamsu da rahoton D. Pertaeus a Majalisar dattawan Amurika

September 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuBg

Majalisar Dattawan Amurika ta fara mahaurori a game da bayyanin da shugaban rundunar sojojin Amurika a ƙasar Irak, ya gabatar mata a jiya litinin.

Yan majalisar, sun nuna rashin gamsuwa da wannan rahoto, wanda ya nuna ci gaban da a ka samu ta fannin samar da tsaro a Irak.

Saidai a nata ɓangare,gwamnatin Irak ta bayyana gamsuwa da jawabin shugaban rundunar Amurika a ƙasar,gaban majalisar Dattawa.

Jannar Petraeus, ya ambata yiwuwar fara janye dakaru dubu 30, daga jimlar sojoji dubu 160 da Amurika ta jibge a Irak.

A cewar mashawarcin gwamnatin Iraki a game da harakokin tsaro, a halin da ake ciki, a kashi 80 cikin 100, sojojin Irak, na iya fuskantar ƙalubalen yan ta´ada.

Mouaffack Al Rubaie ya ci gaba da cewar

Saidai a ɗaya wajen, Al Rubaei ya tabbatar da cewar, akwai sauran rina kaba, a yunƙurin kawo ƙarshen hare-haren ta´adanci, da su ka zama ruwan dare, a cikin wannan ƙasa.