1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IOM za ta mayar da 'yan ci rani gida

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2017

Kungiyar kula da 'yan ci rani ta duniya IOM ta sha alwashin mayar da wasu 'yan ci rani daga kasar Libiya har su 7,000 zuwa kasashensu na asali.

https://p.dw.com/p/2YbP1
Wakilan IOM da 'yan ci rani a Nijar
Wakilan IOM da 'yan ci rani a NijarHoto: DW/

Kakakin kungiyar ta IOM a Libiya wadda keda shalkwata a Tunis babban birnin kasar Tunisiya ne ya tabbatar da wannan kudiri na kungiyar. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar Tarayyar Turai wato EU, ta sha alwashin dakile 'yan ci rani da ke biyo wa ta Libiyan zuwa kasashen Turai, inda a yanzu haka a kwai daruruwan 'yan Najeriya da Nijar da za a mayar gida daga Libiyan. A shekarar da ta gabata ta 2016 ma dai, kungiyar ta IOM ta taimaka wajen mayar da 'yan cirani daga kasashen Senegal da Najeriya da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar kasashensu. Rahotanni sun nunar da cewa sama da 'yan cirani 160,000 ne suka isa Italiya ta teku daga kasar Libiyan da ke yankin arewacin Afirka a shekarar ta 2016 da ta gabata.