1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta sajewar baƙi da yan ƙasar Jamus

November 4, 2010

Gwamnatin Jamus ta ɗauki ƙwararan matakai na inganta zaman baƙi 'yan ci rani a ƙasar.

https://p.dw.com/p/PyHS
Shugabar gwamnatin Jamus da wakilan 'yan kaka-gidaHoto: AP

Gwamnatin Tarrayar Jamus za ta fara wani shirin na baiwa baƙi 'yan ci rani horo, kan sanin ɗabi'u da zaman ta kewar al'ummar Jamus. shirin da aka tsara don inganta sajewar baƙi da jamusawa za'a gudanar da shi ne na zawon shekaru biyar. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana wanna sabon tsarin, inda tace ya zama wajibi bayan shekaru talatin ba' samu cimma nasara kan shirin ƙarfafa sajewar baƙi da 'yan asalin ƙasar ba.

A yanzu haka dai kimanin mutane miliyan biyu ke jiran a basu wannan horon, kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ƙuduri anniyar tabbatar da wannan shirin ya samu nasara, inda ta shaidawa wani taron ingata cuɗayya tsakanin jamusawa da baƙin 'yan ci rani, wanda ya gudana a Berlin, cewa gwamnati za ta bi shirin sau da ƙafa, domin tabbatar da yana tafiya daidai.

Yanzu dai hukumomi sun fahimci cewa dolene sai an samu yin magana kai tsaye, za a iya samun ci gaba shirin. Don haka taron da ya gudana a Berlin shine karo na huɗu da gwamnatin Jamus ke zama tare da ƙungiyoyin baƙi 'yan ci rani dake a ƙasar, inda suke musayar bayanai da gwamnati. Domin tabbat da ƙudurin gwamnati kan baƙi ya cimma nasara, shugar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace.

"Yanzu muna son shirya gudanar da zama na biyar, domin inganta sajewar baƙi abune da zamu bada himma akai. Ɗaukar wani tsarin mai ƙarfi na gaggawa, shine zai bada damar mu sun inda mukayi nasara da inda muka kasa"

Kalaman na Merkel suna nufin nan da shekaru biyar, duk wani baƙo ɗan ci rani ya shiga karatu don koyon al'adun Jamusawa da ma iya harshen Jamusanci.

Muna son ace nan da shekaru biyar zuwa bakwai ɗaukacin mutane dake zama a Jamus. su samu damar shiga wannan shirin karantarwa. Muna ƙiyasin kamar mutane miliyan biyu za su shiga shirin. Muna saran a shekaru biyar masu zuwa, za mu iya cimma abinda ba shimma a shekaru 30 ba"

Tsarin baiwa baƙi horo kan sanin ɗabi'un Jamusawa da nufin ƙarfafa sajewarsu da yan ƙasa, wanda aka ƙaddamar tun shekaru biyar da suka gabata, shine shiri kan baƙi mafi ingaci da gwamnatin Tarayyar Jamus ta yi. Kafin ƙarshen bana, gwamnati na saran kashe euro biliyan ɗaya. kan wannan shirin. Daga cikin abinda za'a maida hankali kuwa zai haɗa da batun kiwon lafiya kamar yadda wakiliyar gwamnati a akan harkar baƙi Maria Böhmer tace....

Batun kiwon lafiya dai wani butune dake da mahimmanci ga manyan gobe daga baƙin 'yan ci rani, wadanda suma tsufa za ta cimmusu. Batu na biyo shine samarwa baƙi ayyukan gwamnati, kamar aikin 'yan sanda da daukarsu a matsayin malaman makarantu, wadanda ke da ilimi kan abinda ya shafi baƙi"

Wasu batutuwan da ake son warwarewa a shirin na gwamnatin Tarayyar Jamus, sun haɗa da tashe-tashen hankula a makarantu da sauran wuraren taruwar jama'a.

Ita dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace samun nasara da rashinta abune da za'a riƙa yin waiway.

Mawallafa: Usman Shehu Usman/Sabine Ripperger

Edita: Umaru Aliyu