Tattalin arziki
Inganta sa'ar fawa
September 6, 2017Talla
Shi dai Sarkin Fawar na Nigeria Alhaji Hamisu Dan Gowon mutum ne mai kaunar ganin matasa sun himmatu wajen neman na kai musamman sana'a wadda sirrin arziki ke cikinta. Don haka ne ya yi wa matasan tushe ta hanyar kafa musu kasuwar dabbobi da mayankunsu har ma da makaranta ta koyon sana'ar fawa.
A wannan mayaka da ya gina a Kano a kalla mutum dubu biyar ake sa ran za su ci moriyarta sannan a kusa da ita akwai babbar kasuwar dabbobi.Alhaji Hamisu Dan Gowon ya yi kira ga duk mai neman arziki ya zo ya ci arzikin ya kuma bar arzikin a gurbinsa.
Ita wannan mayakan da aka yi wa gini na zamani tana da wuraren adana nama da makarantu na Islamiyya da ta koyon sana'ar fawa kuma tun lokacin da aka aza harsashin gininta matasa suke gani a kasa.