1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140510 Deutschland Entwicklungshilfe Wirtschaft

May 15, 2010

Samun bunƙasar tattalin arziki a ƙasashe masu tasowa kamar a ƙasashe masu ci-gaban masana'antu, ya dogara kan daidaita samar da kaya da kuma bukatunsu

https://p.dw.com/p/NOvl
...samar da ruwan sha mai tsabta wani aiki ne mai tsadar gaske...

Tun shekaru 10 da suka gabata Jamus ke ƙoƙarin ganin an samu ci-gaba a wannan ɓangaren ta hanyar gabatar da wasu shirye-shiryen haɗin guiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Yanzu haka dai Jamus ta tallafawa aikin ƙawance har guda 1800, kuma ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Nibel ya ce za a ƙara yawansu.

Gottlieb Hupfer shugaban wani matsakaicin kamfani da ya ƙware wajen tsabtace ruwa, ya ce samar da ruwan sha mai tsabta wani aiki ne mai tsadar gaske a wata ƙasa mai samun matsakaicin ci gaban masana'antu kamar Brazil dake a matsayi na 10 a jerin ƙasashe mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya.

Ko da yake buƙatar tsabtattaccen ruwa a birnin Rio de Janeiro tana da yawa to amma da farko bai samu abokannen hulɗar ciniki a Brazil da za su iya sayen ruwan ba. Amma yanzu abubuwa sun canja bayan an faɗaɗa injin da yanzu haka yake tace gurɓataccen ruwa har lita miliyan 40.

"Mutane 22 dukkansu 'yan ƙasa suke mana aiki bayan mun janye ƙwararrun Jamusawa. Aiki da tare da Jamusawa a Brazil yana da tsadar gaske dake janyo matsaloli. Shi yasa yanzu muna aika Jamusawan don ba da horo na gajeren lokaci, amma sauran aikin 'yan Brazil ke yi. Yanzu haka sun samu ƙarin abokan ciniki. Muna sa rai nan da shekaru biyar za mu fara cin riba."

Hupfer yayi imanin cewa aikinsa ka iya zama mai alfanu ga sauran ƙasashe masu tasowa waɗanda ci-gaban hanyoyin sadarwarsu ba su kai na Brazil ba.

"Tuni mun kai ziyarar ganewa ido a wasu birane a nahiyar Afirka. Da ma dai dukkan aikin da muke yi ya fi ta'allaka a ƙasashe masu tasowa. A can ba a buƙatar kuɗi mai yawa ko abokannen ciniki masu yawa."

Ƙwarewar Hupfer na zaman wata fa'ida ga ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel. Ministan dake goyon bayan tallafawa matsakaitun kamfanonin Jamus, yana jin daɗin nasarorin kamfanonin na Jamus a ayyukan da suke yi a duniya. A bara ma'aikatarsa ta tallafawa ayyukan haɗin guiwa guda 103 da kamfanoni masu zaman kansu, da nufin gudanar da ayyuka masu yawan gaske musamman a ƙasashe masu tasowa, inji minista Dirk Niebel.

"Saboda ƙarancin masu zuba jari a ƙasashe matalauta, muna samun karɓuwa daga hukumomi waɗanda a kullum suke nuna shirin marawa ayyukanmu baya. Kuma idan aka samu sauƙin lamurra, manyan kamfanoni su kan bi sahu."

Minsitan raya ƙasashe masu tasowan na Jamus ya jaddada cewa a kullum sun fi mayar da hankali kan buƙatun ƙasashe da suke ƙawance da su. Ministan yayi watsi da masu zargin gwamnatin Jamus cewa buƙatunta na tattalin arziki kaɗai ta sa a gaba. Ya ce su ba 'yan mulkin mallaka ba ne, ƙawaye ne ga ƙasashe masu tasowa da ke son ƙarfafa haɗin kai tsakani musamman a ɓangaren taimakon raya ƙasa.

Mawallafi: Marcel Fürstenau / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Abubakar Mohammed