1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta harkokin Ilimi a Najeriya

Ibrahim SaniNovember 24, 2007
https://p.dw.com/p/CSdt

Ƙasar Ingila ta yi alƙawarin bawa Najeriya tallafi na Dola miliyan 200, don inganta harkokin Ilimi a ƙasar.Ƙuɗaden za a yi amfani da su ne wajen gina ajujuwan ɗaukar karatu dubu huɗu tare da samar da kayan aiki ga makarantu dubu biyu. Tallafin a cewar rahotanni na daga cikin alƙawarin da Biritaniya ta yi ne na bada Ilimi kyauta ne ga yara,a ƙasashe dake cikin ƙungiyyar renon ƙasar ta Biritaniya. A yanzu haka dai akwai yara miliyan bakwai da ba sa zuwa Makaranta a Tarayyar ta Najeriya. Matakin a cewar masu nazarin yau da kullum, abune da zai taimaka wajen inganta harkokin Ilimi daga tushe a ƙasar.