1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta baiyana jadawalin zaɓe a Najeriya

September 7, 2010

Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da ranaikun gudanar da zaɓɓukan ƙasa a baɗi.

https://p.dw.com/p/P6Rg
Zaɓe a NajeriyaHoto: AP

Hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya tace za'a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 22 ga watan Janairu na shekara baɗi. Kakakin hukumar zaɓen Solomon Adedeji Soyebi ya sanar da hakan yau bayan tsawon lokaci jamaa na ta shaci faɗi game da ranar zaɓen. Kakakin yace zaa gudanar da zaɓen majalisun dokokin tarayya a ranar 15 ga watan Janairu yayin da zaɓen gwamnoni za'a gudanar da shi a ranar 29 ga watan na Janairu. Shugaban ƙasar Goodluck Jonathan wanda ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar bayan rasuwar shugaba Umaru Musa Yar Adua, har yanyu bai fito fili ya baiyana cewa ko zai tsaya takara ba, ko da ya ke dai ana kyautata tsammanin zai yi hakan. Akwai dai taƙaddama a cikin jamiyarsa ta PDP a game da batun karɓa karɓa tsakanin arewaci da kudancin ƙasar.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Yahouza Sadissou Madobi