Indonesiya ta kammala janye dakarunta daga lardin Aceh | Labarai | DW | 29.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indonesiya ta kammala janye dakarunta daga lardin Aceh

A yau ne kasar Indonesia ta janye rundunar karshe na sojojinta su 24,000 daga yankin da tsunami ya lalata na Aceh,wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da zata kawo karshen yakin shekaru 30 tsakanin gwamnati da yan aware na Aceh.

Manjo Janar Supiadin wajen bikin sallamar sojojin yace kimanin sojoji 3,350 zasu koma,a matsayin wani baban mataki na kawo karshen rikici da yayi sanadiyar rayukan mutane 15,000.

Yan tawayen da gwamnati sun koma teburin tattaunawa ne bayan balain ambaliyar ruwa ta tsumanni a wanda ya halaka mutanen 156,000 ayankin na Aceh kadai wasu dubu 500 kuma suka rasa gidajensu.

Yan tawayen sun amince cewa basa bukatar kara munana halin da jamma suke ciki inda suka amince sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan agusta domin kawo karshen rikicinsu da gwamnati.