Indonesiya ta gano gawarwakin mutane 54
August 18, 2015Ma'aikatan ceto na kasar Indunusiya sun bada sanarwar gano a wannan Laraba gawarwakin mutane 54 da suka mutu a cikin hadarin jirgin saman kamfanin Trigana Air Service na kasar na ranar Lahadin da ta gabata . Hukumomin kasar sun bayyana cewa sun gano kuma tarkacen jirgin wanda ya yi day-day a yayin da wani sashensa ya kone kurmus. Sun kuma ce jirgin ya fadi ne a cikin wasu tsaunika masu kuma rukukin itatuwa da ke da wuyar shiga . Abun da ke kawo cikas a kokarin da ake na kwashe illahirin gawarwakin.
Haka zalika sun ce suna ci gaba da neman na'urar nadar bayanai ta jirgin domin sanin takamaiman abunda ya haddasa hadarin. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai jirgin saman kamfanin Trigana Air Service wanda ke aikin jigilar fasinja a tsakanin biranen kasar ya fadi da mutane 54 a cikinsa.
Wannan dai shine karo na ukku a cikin shekara daya da ake samun hadarin jirgin sama a wannan kasa wacce ta yi kaurin suna wajan rashin ingancin jiragen sama da ke sufurin al'umma a kasar