Indonesia da Iran za su gina wata matatar mai a kan tsibirin Java. | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indonesia da Iran za su gina wata matatar mai a kan tsibirin Java.

A yau ne ƙasashen Indonesiya da Iran za su sanya hannu kan wata yarjejeniya, ta gina wata gagarumar matatar mai a kan tsibirin Java da ke ƙasar Indonesiyan. Rahotanni sun ce za a kashe kimanin dola biliyan 5 a kan aikin, wanda za a kammala a cikin shekara ta 2010. Kamfanonin Elnusa da NOIC na Indonesiya da Iran ɗin ne za su ƙulla yarjejeniyar, a lokacin ziyarar da shugaban Mahmoud Ahmadinijad na Iran ke kaiwa a ƙasar ta Indonesiya.

Bisa yarjejeniyar dai, kamfanin NOIC na Iran zai zuba jarin kashi 20 zuwa 25 cikin ɗari a harkar, yayin da kamfanin Elnusa na Indonesiyan zai zuba kashi 20 cikin ɗari, sauran jarin da ake bukata kuma, zai zo ne daga wani tushen.

Ana dai hasashen cewa, kusan kashi 70 cikin ɗari na man da matatar za ta dinga samarwa, za a sayad da shi ne ga ƙasar Sin, yayin da sauran kuma za a yi amfani da shi a cikin gida, wato a ƙasar Indonesiyan, inji wani babban jami’in kamfanin Elnusa na ƙasar. Idan aka gama aikin, matatar za ta iya samada da garwa dubu ɗari 3 a kowace rana. Kamfanin NOIC na Iran dai, ya tabbatar cewa, zai iya bai wa matatar a ƙalla garwa dubu ɗari a kowace rana.