1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

201010 Indien Konflikte

October 20, 2010

Ƙasar Indiya na cikin tsaka mai wuya, kama daga tashe-tashen hankula na cikin gida da ma ƙasashe maƙobtan ta.

https://p.dw.com/p/PjDI
Firaiministan Indiya Manmohan SinghHoto: AP

A yankin Kashmir dake ƙasar Indiya tarzuma sai ƙaruwa take yi a 'yan makwannin da muke ciki, inda ya kasance lokacin da aka fi zubar da jini a tsawon shekarun da yankin ke yi na samun yancin kai daga Indiya. 'Yan aware na yin ƙira ga ƙasar Indiya da Pakistan su jan'ye dakarunsu a ɗaukacin yankin baki ɗaya. Ƙasar Indiya dai tana fiskantar ƙalubale masu yawa, musamman daga maƙobta, ga ƙasar China da ta yi mata fintinkau ta fannin tattalin arziki, a gefe guda kuma ga Pakistan abokiyar gabansu.

"Wani jagoran masu zanga-zanga dake fusace a yankin Kashmir, yana mai cewa 'yancin mu muke buƙata. Batun 'yancin su dai yana nufin samun ƙasar su mai cin gashin kai daga Indiya"

Tashin hankalin da ya haddasa zubar da jini dai ya samu asali ne tun a watan Juni, lokacin da dakarun tsaron Indiya suka harɓe wani matashi har lahira, daganan, tarzuma sai ruruwa ta ke yi kamar wutar daji tun lokacin. Inda matasa suke ƙara nuna fusata da bijirewa.

"Wannan matashin yace ɗauki misali a duk lokacin da mutum ya fito daga gidansa, dakarun Indiya sai su harɓe shi, ya ya kaken ganin lamarin zai ɗore. Waɗannan matasan su ne manyan gobe, sun girma cikin wannan tarzumar. Sunga yadda ake halaka iyayensu, wasu danginsu sun ɓace, ai wannan tamkar ana dafa jinin su ne"

BdT Indien Polizeikräfte werfen mit Steinen nach Protestanten
Sojojin Indiya ke jifan 'yan Kashmir da duwatsuHoto: AP

Fiye da mutane ɗari suka rasa rayukansu a watan jiya kawai cikin yankin na Kashmir. Idan kuma ka yi lissafi tun shekarun 1980 to dubban mutanene suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankalin. Wata ayar da har yanzu ba a bada amsar ta ba, shin yankin Kashmir dake da aksarin mazaunansa musulmaine, shin wa yakamata ya yi iko da shi, Indiya? ko Pakistan? ko kuma a basu yancinsu? Sujaat Buhari wani ɗan jaridane masanin kan rigimar Kashmir.

"Wannan wata siyasa ce mai sarƙaƙiya ga Indiya da Pakistan, ko wacce buƙatun ta na son rai take karewa. Indiya ba za ta jan'ye daga Kashmir ko da taku ɗaya ba, haka itama Pakistan ba za ta daina kare yancin ta a kan Kashmir ba. To sai dai a gefe guda al'ummar Kashmir na son a ware-ware matsalar"

Sai dai tun bayan harin da aka kai a birnin Mumbai shekaru biyu da suka gabata, batun baiwa Kashmir 'yancin kai samu koma baya, inda aka rufe batun baki ɗaya, domin Indiya na zargin 'yan ta'andan sun samu goyon bayan Pakistan. Farfesa Raja Mohan, wani masanin siyasar ƙasa da ƙasa ne

"A halin yanzu Pakistan na tsaka mai yuwa, bayan ambaliyar ruwa da ta tsiyata yan ƙasar, gwamnatin farar hula dake mulki bata da iko kan sojojin ƙasar, kuma mutun bai son dawa zaka iya tattaunawa ba. Don haka banga yadda za'a iya samun masalaha ba"

Indiya dai yanzu tana tsaka mai wuya, a gefe ɗaya ta yi iyaka da abokiyar gabar ta Pakistan wanda ta mallaki makaman nukiliya, a ɗaya hannun maƙobciyar ta wato China ta zuba jari mai yawa a ƙasar. Ita kuwa ƙasar Amirka sai ƙara neman ƙulla hulɗa da Indiya ta ke yi, don rage tasirin China a yankin Asiya. Ga shi Indiya na son ci-gaba da hulɗa mai tarihi dake tsakanin ta da ƙasar Rasha.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Kai Küstner

Edita: Mohammad Nasiru Awal