India ta yi gwajin makamai masu linzami | Labarai | DW | 19.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

India ta yi gwajin makamai masu linzami

Kasar India ta ce ta yi nasarar gwajin makamai masu linzami amma masu gajeren zango wadanda ke iya daukar makamin nukiliya. Wani jamií a maáikatar tsaro ta kasar ya ce makamin mai linzami wanda aka yiwa lakabi da Prithvi an gudanar da gwajin sa ne daga wata cibiya a gabar kogi a yankin Jihar Orissad dake gabashin kasar. Wannan gwajin dai ya zo ne kwanaki uku kacal bayan da kasar Pakistan ta gudanar da makamancin sa wanda ta yiwa lakabi da Hatf 5.