Inda aka kwana bayan mace macen love parade
July 27, 2010A tarrayar Jamus, shugabannin siyasa sun fara sukan magajin garin Duisbourg dangane da kunnen uwar shegu da yayi da gargaɗin da aka yi masa na illar da ke tattare da bikin Love Parade. Mutane 20 ne daga asabar zuwa yanzu suka rasa rayukansu biyowa bayan turereniyar da cunkoson jama'a ta haifar a bikin na sheƙe aya na matasa.
Hukumomi na ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da alhakin turereniyar da ke ci gaba da fiskantar suka daga al'ummar ta Jamus. Shugabannin siyasa na ci gaba da zargin waɗanda suka shirya bikin da ya sa dubban matasa kwarara a garin da kwata-kwata yawan al'umanta bai haura dubu 500 ba.
Ɓangarori da dama na ci gaba da kira ga magajin garin birnin na Duisburg da ya yi murabus. Ranar asabar ne za a gudanar da taron addu'o'i da shugabar gwamanti wato Angela Merkel za ta katse hutunta domin halarta.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Ahmed Tijjani Lawal