Ina aka kwana game da rikicin siyasa a Burma | Labarai | DW | 27.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ina aka kwana game da rikicin siyasa a Burma

Wakilin Mdd na musanman a kasar Burma ya bukaci gwamnatin kasar data koma teburin sulhu da shugabar adawa ta kasar. A cewar Ibrahim Gambari, ci gaba da tattaunawar sulhu a tsakanin San Suu Kyi da bangaren gwamnati, abune da zai taimaka wajen warware rikici na siyasa da kasar ta fada a ciki. Duk da kiraye kiraye da kasashen duniya keyiwa gwamnatin ta Burma, har yanzu mahukunta na kasar na ci gaba da tsare yan adawa na kasar. Yan adawar dai na muradin saka kasar ta Burma ne a tafarki na dimokradiyya, bayan wani tsawon lokaci da kasar tayi karkashin mulkin soji.