In an jima za´a kammala taron Majalisar Dinkin Duniya akan AIDS | Labarai | DW | 02.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

In an jima za´a kammala taron Majalisar Dinkin Duniya akan AIDS

Mahalarta babban taron MDD kan cutar AIDS ko SIDA a birnin New York sun amince da daftarin wani kuduri da aka tabka zazzafar muhawwara akai, wandan zai kasance wani makamin yaki da yaduwar wannan cuta a duniya. Ana sa rai a wani lokaci yau din nan babbar mashawartar MDD zata albarkaci kudurin, wanda zai ba da damar yin kandagarki da cutar ta AIDS, samar da magungunanta da kula da masu dauke da ita kafin shekara ta b2010. A lokacin da yake yiwa taron jawabi babban sakataren MDD Kofi Annan ya bayyana cutar ta AIDS da zama babban kalubale a wannan zamani da muke ciki. Annan ya yi kira da a kara yawan kudaden da ake zubawa a asusun yaki da yaduwar kwayoyin HIV daga dala miliyan 8.3 a bara zuwa dala miliyan 20 a shekara ta 2008. Tun bayan gano bullar ta a shekarar 1981, AIDS ta halaka mutane sama da miliyan 25.