In an jima shugaba Bush zai gana da hafsoshin sojin Amirka akan Iraki | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

In an jima shugaba Bush zai gana da hafsoshin sojin Amirka akan Iraki

A dangane da karuwar tashe tashen hankula a Iraqi, a wani lokaci yau shugaban Amirka GWB zai gana da manyan hafsohin sojin Amirka akan halin da ake ciki a Iraqin. Majiyoyin fadar White House sun ce kwamandan sojin Amirka a Iraqi George Casey da kwamandan sojin Amirka a GTT John Abizaid na daga cikin wadanda zasu halarci taron. Kakakin Bush, Tony Snow ya ce tun wasu makonni da suka wuce aka shirya gudanar da taron saboda haka yin shi a yau bai da wata alaka da rincabewar halin da ake ciki a Iraqin a yanzu. A cikin wannan wata kadai Amirka ta yi asarar sojoji fiye da 70 a Iraqi. A wani mataki na neman goyon bayan jama´a gabanin kuri´ar ´yan majalisun dokokin Amirka da zai gudana kwana-kwanan nan shugaba Bush cewa yayi.

“Daya daga cikin muhimman batutuwa na wannan zabe shi ne wanda zai fi iya hangen nesa kuma zai fi iya zama cikin shiri don tinkarar abin da ke tafe. Hanya mafi muhimmanci da Amirka zata bi don kare kanta ita ce ci-gaba da wannan matakin da take dauka.”