1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar wutar daji a Rasha

August 11, 2010

Greenpeace ta yi gargaɗi game da asara da wutar daji za ta haifar a Rasha.

https://p.dw.com/p/OiX7
Hoto: AP

ƙungiyar Greenpeace  ta yi kira ga hukumomin Rasha da su ninka matakan da suka ɗauka domin hana wutar daji da ke addabar ƙasar isa cibiyar haɗa sinadarin nukuliya ta Chernobyl. Wannan ƙungiya da ta himmatu wajen alkinta muhalli a duniya, ta ce wutar ta daji na barazana  ga makomar cibiyar da ma dai mazauna garin.

Ma'aikatar da ke kula da ayyukan jin ƙai ta Rasha ta ce ana ci gaba da fiskantar tashin gobarar a yankin yammacin ƙasar. kana ta bayyana cewa za a ci gaba da fuskantar gurɓacewar yanayi sakamakon ƙaruwar zafi da ruruwar wutar jeji cikin kwanaki 10 masu zuwa.

 Wannan zafin ya na barazana ga gonakin alƙama da aka noma a wannan shekara. Tuni dai hukumomin Rasha dake zama ƙasa ta uku da ta fi arzikin alkama a duniya ta dakatar da fitar da wannan haja zuwa kasuwannin daban-daban.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu