Illar canjin yanayi kan abinci da gudun hijira | NRS-Import | DW | 18.11.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Illar canjin yanayi kan abinci da gudun hijira

Illar da canjin yanayi ke da shi ga batun gudun hijira da rashin abinci abu ne mai tsoratarwa.

default

Matsalar canjin yanayi

Bincike ƙalilan ne ake gudanarwa game da dangantaka tsakanin canjin yanayi da ƙaurar jama'a. To sai dai kuma gaskiyar abin shi ne ,matsaloli na yanayi zasu ƙara nauyi kan ƙasashe masu tasowa cikin shekaru masu zuwa, inji Jeni Klugman wadda ta wallafa rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya kan ci gaban ƙasashe.

"yadda canjin yanayi ke tilasta yin ƙaura, batu ne da ya kamata a duba shi. Haka kuma a duba alal misali batun kwararowar hamada na kara talauci. A darfur alal misali canjin yanayi na kara matsalolin da jama'a ke ciki tare da tilasta masu ƙaura da kuma sauran dinbin batutuwa"

Cikin rahoton Jeni Klugman ta baiyana wasu abubuwa dabam da zasu iya faruwa. masana kimiya sun yi hasashen cewa nan da shekaru 10 masu zuwa kusan rabin filayen noma a nahiyar Afurka zasu bushe. haka zalika Klugman tace ambaliyar ruwa zata lalata anfanin gona a yankuna dake da tsaunuka a Asiya da Latin Amurka. Lalacewar filayen noma na ɗaya daga cikin ababen dake haddasa ƙaura inji Aderanti Adepoju na cibiyar binciken kan ƙaura da baƙi na Najeriya.

"lalacewar muhalli, zaizayar kasa, ambaliya da sauransu, duk dalilai ne, haka kuma daya daga cikin manyan dalilan dake sanya kaura sakamakon lalacewar muhalli shine manufofin kasashen yamma, inda suke baiwa manaomansu rangwame amma a tsawwala haraji kan albarkatun noma na Afurka, wadda noma shine kashin bayan jamaÄar Afurka da Asiya da Latin Amurka. saboda haka idan aka samu lalacewa muhalli tilas wadannan mutane su kaura zuwa birane"

Bincike ya nuna cewa mutane tsakanin miliyan 200 zuwa biliyan guda ne canjin yanayi zai tilastawa barin yankunansu ko ma ƙasarsu baki ɗaya. Ƙasashen da ke cikin haɗarin faɗawa wannan matsala kuwa sune ƙasashen Afurka da wasu ƙasashe a gabaci da kudancin Asiya. Ƙasar Bangladesh alal misali ta kasance ne cikin wani kwari dake tattare da haɗarin samun ambaliya daga teku. Bincike ya nuna cewa tuni an fara samun ƙaura daga wuraren da ambaliya ta fara shafa. Syed Saiful Haque jami'i ne na gidauniyar raya ƙasar ta Bangladesh.

"a bara mun samu manyan ambaliya sau biyu, jama'a har yaanzu suna acikin wahala, ba zasu iya komwa gidajensu ba, binciken da muka yi ya nuna cewa wasu ne kokarin sayarda filayensu na noma don su koma birane ko ma wasu kasashe dabam"

A cewar rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya mutane kusan miliyan 145 ne suke cikin barazanar ambaliyar teku. sabaoda haka wakilan ƙasashe masu tasowa sun bukaci ƙasashe da suka ci gaba da su taimaka masu wajen yaƙi da canjin yanayi. A hannu guda kuma su nemi nemi kare hakkin baƙi da ke ƙaura zuwa turai sakamakon canjin yanayi a ƙasashensu. A ɗaya hannun kuma alal misali mutane kamar Muhammad Rashed Al Hassan ɗan ƙasar Bangladesh suna bukatar taimakon kuɗi ga ƙasashensu.

"babban dalilin hakan kuwa shine kasashe da suka ci gaba sune ummul aba'isin dumamar yanayi , ko da a watannin baya mun samu ambaliyar ruwa inda muka yi hasara na kusan dala biliyan daya da dama suka rasa matsuguni, saboda haka yana da wuya ga kasarmu ta taimakawa wadannan mutane, muna bukatar taimako don tsugunad da wadannan mutane su ci gaba da rayuwarsu "

Batun yadda za a bullowa canjin yanayi har yanzu shi ne batu da ake sabani kansa wajen taro kan canjin yanayi. Ƙasashe masu tasowa dai basu yi wasu alkawura ba. ga ƙasashe da suka ci gaba kuma waɗanda kuma canjin yanayin ya fara shafa , batun shi ne na samun ƙwararan alkawurra da kuɗaɗe da za a ɗauki matakan magance matsalar. Ƙasashe 100 da canjin yanayi ya fi shafa sune ke da alhakin fitar da kashi uku% kaɗai cikin 100 na hayaƙin masana'antu masu guba a duniya.

Mawallafi: Hauwa Abubakar Ajeje

Edita:        Zainab Muhammad Abubakar

 • Kwanan wata 18.11.2009
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/KaD0
 • Kwanan wata 18.11.2009
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/KaD0