Illar ambaliyar ruwa a Pakistan | Labarai | DW | 03.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Illar ambaliyar ruwa a Pakistan

Mutane milioyn biyu da rabi na ci gaba da fiskantar raɗaɗin ambaliyar ruwa da ya addabi ƙasar ta Pakistan.

default

Yawan mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa mafi muni da ta afka ma ƙasar  Pakistan ya tasamma 1500. ƙungiyar agaji ta Red Cross ko kuma croix rouge ta nunar da cewa aƙalla mutane miliyon biyu zuwa uku ne suke cikin barazanar kamuwa da cutar kwalara sakamakon ribtawar ƙasa da kuma ambaliya da wasu sassa ƙasar ke ci gaba da fiskanta.

 Jami'an agaji na ci gaba da cin karo da ƙalubale biyowa bayan lalacewar hanyoyi da kuma rushewar gadoji. kakakin hukumar MDD da ke kula da ayyukan jin ƙai wato Nicki Bennett ya ce ƙarancin ruwan sha mai tsafta da ake fiskanta na daɗa jefa rayukan dubun dubatan mutane cikin halin rashin tabbas.

Kiyasin MDD ya nunar da cewa mutane sama da rabin miliyon sun yi asarar matsugunansu ya zuwa yanzu. Masu hasashen yanayi sun nunar da cewa  za a ci gaba da samun ruwan sama kaman da bakin ƙwarya a wasu yankunan ƙasar ta Pakistan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar