1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ilimin Zamantakewa—Duniya cike da abubuwan mamaki.

Zainab MohammedJanuary 22, 2009
https://p.dw.com/p/DrEr

Ilimin Zamantakewa—Duniya cike da abubuwan mamaki.

Duniyar nan tamu na cike da abubuwan mamaki waɗanda ba ma la’akari da su.

Alal misali, ba kowa ne ya san yadda saƙon kar ta kwana wato “text” a turance, wanda aka aika daga wayar salula ke samun mutumin da aka aikawa ba. Haka zalika ba kowa ya san dalilan da suka sa Bature ya ƙera taya ta zama launin baƙa ba.

Shirin Ji Ka Ƙaru zai yi nazari ne akan abubuwan mamaki dake tare da mu, ba lalle sai wanda aka koya a makaranta ba. Misali masu kawo mana rahotanni sun binciko yadda ake yin leda da kuma illa ko illolin da take kawowa na gurɓata muhalli.

Abubuwan jan Hankali.

Shirin zai nuna yadda mutane ke ƙaunar junansu da kuma yadda dabbobi ke zaune a muhallansu ba tare da muzgunawa ba. Za mu kuma duba dalilan da suka sa ko me ya sa dankali ke yin taushi in an dafa, a yayin da shi kuma ƙwai ke daskarewa ya yi tauri in an dafa. Shi ya sa aka ce ilimi tumbin giwa, Shirin Ji Ka ƙaru zai fayyace muku komai.

Za a iya sauraron shirin a cikin harsuna shidda, wato a harsunan Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese da Amharic.

Ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus ya taimaka aka yi wannan shiri na Ji Ka Ƙaru.