1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ikon shugaban Najeriya

Halimatu AbbasSeptember 19, 2012

Tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar ya nemi rage karfin ikon shugaban kasa a matsayin hanyar kaiwa ga tabbatar da inganci ga siyasa dama harkoki na zamantakewa a tsakanin al'ummar Najeriya.

https://p.dw.com/p/16BfK
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Hoto: picture alliance / dpa

.

A na dai yi masa kirari irin na mai cikakken iko. Ya kuma kai ga yanka zaki da daci a cikin kusan shekarunsa 35 yana aiki a Tarrayar Najeriya.To sai dai kuma sannu a hankali gazawarsa na fitowa da daukar hankali a Tarrayar Najeriyar da wasu daga cikin 'ya'yanta ke neman sauyi ga tsarin shugabban kasa mai cikakken ikon da kasar ke tafiya kai yanzu.An dai ruwaito tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar na neman rage karfin tsarin da ya dauki shugaban kasar zuwa kololuwar iko amma kuma ake ta'allakawa da matsalolin siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewar da kasar ta Najeriya ke fuskanta yanzu haka.

Atiku bai fito karara ba

Duk da cewar Atikun bai fito ya bayyana aniyarsa ta mika bukatar gyaran ga majalisun tarrayar da yanzu haka ke shirin sabon gyara ga kundin tsarin mulkin kasar ba, sabon matsayin daga dukkan alamu ya kama hanyar sosa ran yan siyasa dama sauran masu ruwa da tsaki da kokarin Tarrayar Naeeriyar na ci-gaba. Barrister Abubakar Mallami dai na zaman babban mashawarcin shari'a ga jam'iyyar CPC mai adawa a Tarrayar Najeriya. To in har karatun na zaman na kuskure ga dan uwansa Baba Dala da shi kuma ke zaman tsohon mashawarcin na shari'a ga jam'iyyar PDP mafita kawai na zaman fadawa kai gaskiya a cikin tsarin fedaraliyyar da kasar ta Najeriya ke ikirarin bi yanzu haka.

Babu wata matsala game da tsarin shugaba mai cikakken iko

A shekara ta 1979 ne dai kasar ta Nigeria ta fara amfani da tsarin da ta aro a kasar Amirka kuma ta ce zai jagoranci harkoki na siyasa da zamantakewar al'ummarta. Tsarin kuma da ya mika dimbin iko kan harkokin da suka shafi tsaro da zamantakewa da albarkatun kasa da ma ragowar harkoki na yau da gobe ga shugaban kasar ta Nigeria. Tsarin kuma da a cewar Dr. Hussaini Audu da ke zaman shugaban cibiyar inganta harkokin rayuwa ta Action Aids ba shi da wata matsala a kashin kansa. Kowane lokaci daga yanzu ne dai majalisun tarrayar Najeriya suka ce suna shirin duba duk wata bukatar gyara ga kokarin tabbatar da tsari na gari a tsakanin a'lummar kasar.

Zaku iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Halima Balaraba Abbas