ICC ta sake ba da sammacin shugaba Omar Hasan Al-Beshir | Labarai | DW | 12.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC ta sake ba da sammacin shugaba Omar Hasan Al-Beshir

Kotun hukunta manyan lefikan yaƙi wato ICC,ta zargi shugaban Sudan Omar Hasan El-Beshir da aikata kisan kiyasu a yankin Darfur, ta kuma bada sammacin sa.

default

Ko Omar El-Beshir zai shiga hannun kotun ICC ?

Kotun hukunta manyan lefukan yaƙi dake birnin the Hague ko kuma La Haye ta sake ba da sammancin shugaban ƙasar Sudan Omar Hasan El Beshir.A wannan karo, kotun na tuhumar sa da aikata lefin kisan ƙare dangi a yankin Darfur

A watan Maris na shekara bara, kotu ta ba da sammacin farko ga Al Bashir, sai dai har ya zuwa wannan lokaci ya musanta zargin da ake yi masa.

Fiye da mutane dubu ɗari ukku ne su ka rasa rayukansu a yankin Darfur a sakamakon tashe- tashen hankula da su ka ɓarke.

`Yan tawayen Darfur sun danganta wannan saban sammaci a matsayin wata gagaramar nasara.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Halima Balaraba Abbas