1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC: Al Faqi zai biya diyyar hubbaren Timbuktu

August 17, 2017

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta fito da sakamakon hukuncin kan mai kaifin kishin addinin nan dan kasar Mali Ahmad Al-Faqi Al-Mahdi wanda ya rusa hubbaren waliyai na birnin Timbuktu.

https://p.dw.com/p/2iPUu
Ahmad Al Faqi Al Mahdi Prozess Den Haag Strafgerichtshof Weltkulturerbe
Hoto: picture-alliance/dpa/P.Post

Kotun da ta yi zama kan batun a wannan Alhamis, ta ci Ahmad Al Faqi tarar euro miliyan biyu da dubu 700 a matsayin kudin ta'adin da ya yi.  Alkalin kotun Raul  Pangalangan, ya ce ta la'akari da barnar da Al Madi ya aikata wa daidaiku da ma bakin dayan al'umar Timbuktu da na duniya, Kotu ta dora maka tarar euro miliyan 2.7, wanda ke matsayin diyya da za a bai wa dukkanin bangarorin da wannan barna ta ka ta shafa.

Wannan dai shi ne karo na farko da kotun ta ICC za ta dauki irin wannan mataki a cikin shari'ar da ta shafi lalata kayan tarifi. A watan Satumbar bara ne dai kotun ta yanke hukuncin zaman jarum na shekaru tara kan Ahmad al-Faqi. A shekara ta 2012 lokacin mamayar da kungiyoyi masu da'awar jihadi suka yi wa arewacin Mali, Al Faqi ya jagoranci aikin rusa wasu hubbaran waliyyai na Timbuktu wanda ke cikin jerin kadarorin duniya na hukumar kula da dabbaka al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya.