1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ibtila'in Saliyo da Burkina sun dauki hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
August 18, 2017

Harin ta'addanci da aka kai a wani gidan abinci na wasu Turkawa ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Ougadougou da asarar daruruwan rayuka a Saliyo da nasarar ceto jariri daga cutar HIV su ne jaridun suka duba.

https://p.dw.com/p/2iTAm
Burkina Faso Tag nach dem Angriff in der Kwame Nkrumah Avenue in Ouagadougou
Hoto: picture-alliance/abaca/AA/O. De Maismont

A sharhunan jaridun na Jamus za mu fara ne da jaridar die Welt wanda ta bayyana cewa a kasar Burkina Faso an sake samun harin ta'addanci. Harin wanda aka kai a wani gidan cin abinci mallakar wasu turkawa ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Kawo i yanzu dai babu tabbacin wadanda suka kai wannan harin, sai dai a watan Junairu shekara ta 2016, wasu 'yan ta'addan sun kai makamancin wannan hari, inda suka auna wani Otel da baki masu yawon bude ido ke sauka abin da ya kai ga mutuwar mutane 30. A wancan lokacin kungiyar Alka'ida a yammacin Afirka da kasashe Larabawan arewacin Afrika, ita ce ta dauki alhakin kai harin. Burkina Faso ta samu kanta cikin tsaka mai wuya inda kan iyakarta da Mali mai cike da hamada ke da wahalar lura da masu shiga ko fita, gashi kuma lamarin na faruw ne a dai-dai lokacin da gwamnatin kasar ke kokarin karfafa matakan demokuradiyya biyo bayan kifar da gwamnatin kama-karya ta Blaise Compaoré wanda ya yi shekaru sama da 20 yana mulki.

Barnar ambaliya a Saliyo

Erdrutsch in Sierra Leone Sicherheitskräfte  Schutzmasken
Hoto: picture-alliance/AP/M. Kamara

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemein Zeitung, ta yi sharhinta ne kan ibtila'in da ya aukawa kasar Saliyo, inda ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane. Akasarin wadanda suka mutu dai laka ce ta rufe su bayan ruftawar gidaje. Kawo i yanzu babu cikakkun alkaluman yawan wadanda suka mutu, koda yake hukumomi na cewa kimanin mutane 312 ne suka mutu, yayin da wasu na cewa yawan wadanda suka mutu ya haura mutane 500. An dai yi zargin cewa sare bishiyoyi da aka yi a wani yanki na Freetown babban birnin kasar don gina sababbin gidaje, yana daga cikin abin da ya haddasa mumunar ambaliyar ruwa.

Alamun nasara a yaki da cutar HIV

Kinder und Aids, Aids Waisen in Südafrika
Hoto: dpa

An samu nasara warkar da wani jariri da aka haifa da kwayar HIV a kasar Afirka ta kudu. Wannan shi ne labarin jaridar Berliner Zeitung, wacce ta ce wannan labari mai kyau ne ga duniya baki daya. Domin an yi shekaru da dama ana neman maganin cutar HIV wacce ta kashe dubban mutane amma ba a kaiga samun nasara ba. Jaridar ta ce a wani taron kasa da kasa da ya gudanan a Paris aka fidda wannan sanarwa ta cewa, an haifi jaririn da da kwayar HIV amma likitoci suka dage da bashi magungunan karya garkuwar cutar HIV wanda kuma yanzu bincike ya tabbatar cewa jaririn bayan watanni tara baya dauke da cutar kwat-kwata.