1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ibrahim Gambari ya gana da hukumomin Burma

Wakilin mussaman na Majalisar Ɗinkin Dunia a ƙasar Burma kokuma Myanmar Ibrahim Gambari, ya sake komawa wannan ƙasa, a yunƙurin sa, na lalubo bakin zaren warware rikicin da ta ke fuskanta.

A safiyar yau, ya gana da ministan harakokin wajen Myanmar, da kuma ministan ƙwadago Aung Kyi, wanda gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta naɗa, a matasyin mai tattanawa da shugabar yan adawa, Aung San Suu Kyi.

Ziyara ta Ibrahim Gambari, itace ta 2, tun bayan da ƙasar Myanmar ta tsinci kanta, cikin tashe-tashen hankulla a watan Satumba da ya wuce.

Saidai kuma ziyara na wakana, a lokacin da Gwamnatin mulkin soja ta yanke shawara kawo ƙarshen zaman shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia, Charles Petrie a ƙasar.

Hukumomin Burma na zargin sa, da wuce gona da iri, da kuma shiga sharo ba shanu, a harakokin ta, na cikin gida.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Dunia ya bayyana takaici, a game da wannan mataki, ya kuma jaddada goyan bayansa, ga Charles Petrie, wanda ke jagorancin tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a Burma tun shekara ta 2003.