IAEA tayi gargadi adangane da kaiwa Iran hari | Labarai | DW | 17.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IAEA tayi gargadi adangane da kaiwa Iran hari

Shugaban hukumar kula da yaduwar nuclear ta mdd yayi gargadi dangane da afkawa Iran da hari ,kamar yadda akayi wa Iraki,tare dacewa hakan zai iya kasancewa ne kadai a mataki na karshe,da komitin sulhun zata iya zartarwa.A martaninsa dangane da gargadin Faransa na cewa ,duniya ta kasance cikin shrin kota kwana idan Iran ta mallaki makaman Atom,Mohammaed Elbaradei yace bazai shiga kowace mahawara adangane da kaiwa iran hari ba.Ya jaddada cewa komitin sulhun mdd ne kadai yake ikon zartar da haka,inda yayi kira ga kasashen duniya dasu duba kasar Iraki da halin da suke ciki,kafin su kai hari makamancin wannan akan kowace kasa.