Husufin rana a sassan kasashen duniya | Labarai | DW | 29.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Husufin rana a sassan kasashen duniya

A yau ake sa ran aukuwar Husufin rana ko kuma dare biyu a sassa da dama na duniya. Masana kimiyar sararin samaniya tare da yan yawon bude idanu sun fara hallara a wasu rukunan wurare domin ganewa idanun su Husufin ranar. Husufin zai fi baiyana ne sosai a kasar Libya dake arewacin Afrika inda a yanzu haka jamián cibiyar binciken sararin samaniya ta kasa da kasa NASA suka isa kasar domin ganewa idanun su yadda husufin zai auku. An baiyana cewa Husufin zai dauki tsawon mintina bakwai ne kacal. Kasashen dake kan daírar inda husufin zai auku sun hada da Gahana da da Togo da jamhuriyar Benin da Nigeria da Niger da Libya da kuma Masar, sauran sun hada Turkiya da Georgia da Rasha da Kzakhstan da kuma Mongolia. Masana kimiya sun gargadi jamaá da su kiyayi kallon rana kai tsaye a yayin husufin domin yana iya yiwa idanun su lahani. Tuni dai wasu kasashe suka samar da tabarau na musamman ga jamaá don kare hasken ranar. Masana kimiya sun baiyana cewa a kan sami husufin rana sau daya bayanan watanni 18. Masu binciken sararin samaniya sun yi hasashen aukuwar husufin rana ta gaba, a ranar 1 ga watan Augusta na shekarar 2008.