Husufi mafi tsawo a duniya | Amsoshin takardunku | DW | 12.02.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Husufi mafi tsawo a duniya

Taƙaitaccen bayani game da Husufi mafi tsawo da aka sani a tarihi

default

Zazzaɓin rana

Masu saurarommu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.


Tambaya: Don Allah filin amsoshin takardunku, ku sanar da ni Khusufi mafi tsawo da aka taɓa yi a duniya ? Ni ce Mariya Aminu, daga birnin Lome, na ƙasar Togo.


Amsa:Khusufi dai ya kasu kashi biyu. Akwai Khusufin rana, da akance da shi (Solar Eclipse ) da turanci, da Hausa kuma amfi kiransa da suna Zazzaɓin rana; wanda kuma akasarin lokuta akan ce dashi Wata ya kama rana. Na biyu kuma shi ne Khusufin Wata amma dai a Hausance am fi ambatonsa da suna Zazzaɓin wata, wato (Lunar Eclipse) da turanci, wanda kuma akasarin lokuta akan ce rana ta kama wata.


To kafin ace an fuskanci Zazzaɓin Rana, sai idan wata ya ratsa tsakanin sararin duniya da kuma rana. A tarihi dai an fuskanci zazzaɓin rana ne mafi tsawo a shekarar 1955, wanda kuma ya ɗauki tsawon mintoci 7, da daƙiƙa 31. To amma zazzaɓin rana mafi tsawo wanda ya auku a ƙarni na 20, ya kasance ne a ranar 30th ga watan Yuni na 1973
Zazzaɓin rana wanda ya auku mafi tsawo a baya-bayan nan shi ne wanda aka yi shi ranar 11, ga watan Yuli na 1991, inda ya ɗauki tsawon mintuna 6, da daƙika 54.b Kuma ana sa ran cewar za a kuma fuskantar wani zazzaɓin rana mai tsawo a ranar 22 ga watan Yuli na 2009, wanda zai shafe tsawon mintuna 6, da daƙika 40


To idan muka koma ga kusufin wata kuwa, sai mu ce, Shi zazzaɓin wata ya na faruwa ne a lokacin da Duniya ta ratsa tsakanin Wata da Rana, kuma kusufin wata mafi tsawo da aka sani a tarihi shi ne wanda ya auku a ranar 31 ga watan Mayu a Shekarar ta 318, inda wannan kusufi ya ɗauki tsawon Awa 1 da minti 47 da daƙiƙa 14.