Husa´o´in soja na Barack Obama | Siyasa | DW | 18.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Husa´o´in soja na Barack Obama

Shugaba Barack Obama ya roƙi amurikawa su ƙara haƙuri agame da aiyukan sojojin Amurika a Afganistan da Irak

default

Jawabin B.Obama game da aikin sojojin Amurika a Afganistan da Iraki

Shugaban Amirka Barak Hussain Obama, yayi kira ga Amirkawa dasu ƙara haƙuri dangane da zaman sojojin ƙasar a Afganistan,tare da cewar aikin wanzar da tsaro da kuma zaman lafiya ba abune da za'a samu cikin ƙanƙanin lokaci ba.

A lokacin jawabin da yayi, shugaba Barak Obama ya jajjadawa amirkawa irin ƙoƙarin da Amirkan keyi na yaƙi da wa'yan da ya kira 'yan ta'ada da kuma 'yan Taliban dana Al'ƙaida dake da sansanoni dabamdaban a yankin ƙasar ta Afganistan.

Don haka Shugaban na Amirka, sai ya ƙara da cewa:sabbin matakan da muke ɗauka suna da manufa dake cike da burika na samun nasara,wanda shine na dagulawa da kuma gamawa da ɗokacin aiyukan al-ka'ida da sauran magoyan bayanta a duk inda suke.

Kuma ya kamata amirkawa su sani cewar,wannan yaƙi da mukeyi ba yaƙi ne na ganin dama ba,yaƙi ne da ya zama wajibi a gare mu,domin hana aukuwan abinda ya faru na harin 11 Satunba,domin kuwa irin wayannan ƙungiyoyi na aAl-ƙa'ida da Taliban a shirye suke, su sake kai mana harin idan ba'a magance su ba.

Don haka shugaba Obama ya nunar da buƙatar haƙuri daga ɓangaren amurkawa a tsawon shekarun da sojojin Amirkan zasu shafe a Afganisatan, wajen yaƙi da 'yan ta'adda,faɗan da kuma yanzu yace ana fuskantar matsalolin gaske don haka nema Amirka zataci gaba da maida hankali akai,ba tare da la'akari da sakamakon zaɓen da za'a gudanar a Afganistan ba.

Daya juna akan batun halin da sojojin Amirka ke ciki a Iraƙi kuwa, shugaban na Amirka ya shedawa tsofin sojin na Amirka cewa: a ƙarshen shekara ta 2011 ne Amirkan zata yanje dokacin sojojin ta daga Iraki,abin da kuma zai kawo ƙarshen mamayar sojojin Amirkan a wanann ƙasa"

Tun bayan harin da aka kai ƙasar Amirka 11 ga watan Satunban shekara ta 2001 ne dai, Amirka ta mamaye Afganistan tare da kifar da gwamnatin Taliban da take zargi da marawa ƙungiyar Al'kadida data ɗauki alhakin harin na Amirka baya.

Inda daga bisa ni kuma Amirka, ta faɗaɗa mamayan ta akan Iraƙi da sunan gano makamai masu guba da tace tsohon shugaban Iraƙin Saddam Hussain ya mallaka.

Wannan mamaya da Amirka tayi a Iraki ya haifar da hasarar dubban sojojin Amirka,lamarin daya sanya amirkawa dawowa daga rakiyar gwamnatin Republican ta tsohon shugaba G.Bush da tace tana yaƙi da 'yan ta'adda.Damar da ake ganin Shugaban Obama yayi amfani da ita, na alƙawartawa amirkawa dawowa da sojojinsu gida, muddin suka zaɓe shi shugaban Amirka.Alƙawarin da kuma tuni ya fara cikawa.

Mawallafi: Babangida Salisu Jibril

Edita: Yahouza sadissou