1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hurucin Kondalisa Rice a game da rahoton kissan Raffik Harriri

October 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvO7

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Kondolisa Rice, ta ce ba ta kwankwanto, kasashen dunia za su bada hadin kai, ga Amurika, domin daukar matakan ladabtar da kasar Syria, da a ka samu da hannu dumu dumu, a cikin kissan gillan da a ka yi wa tsofan Praministan Labanon Raffik Hariri, a watan Februarun da ya gabata.

Rice, ta yi wannan kalamomi kwanaki 3, bayan da komitin da Majalisar Dinkin Dunia ta girka, ya gabatar da rahoton sa, a kan bincikne da ya gudanar, a game da wannan kissa.

Tun ranar juma´a da ta wuce ,Amurika ta bukaci shirya taron gaggawa na komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia domin bayyana matsayin sa a game da sakamakon wannan bincike.

Tunni, Amurika ta samu goyan baya daga Britania, inda sakataran harakokin wajen kasar, Jack Straw, ya bayyana ra´ayin da ya zo daidai, da na gwamnatin Amurika.

A nata gefe kasar Syria, ta rubuta wasiku ga kasashe membobin komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia,domin bayyana rashin amincewa, da sakamakon wannan rahoto, mai cike da kage, da shafa kashin kaji, ga hukumomin Syria.