Hurucin Jose M. Barosso a game da taron AU -EU na watan desember 2007 | Labarai | DW | 09.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hurucin Jose M. Barosso a game da taron AU -EU na watan desember 2007

Shugaban hukumar zartaswa ta ƙungiyar gamayya turai, Jose Manuel Barosa ya yi tsokaci a game da taƙadamar da ta kuno kai, wattani 2 kaccal ,kamin buɗa taron Eu da ƙasashen Afrika a birnin Lisbonne na ƙasar Portugal.

A wani jawabi da ya gabatar, watan da ya wuce, praministan Britania Gordon Brown, ya nunar da cewa, ba za shi halarci wannan taro ba, tare da shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe.

A jiya ma, Brown ya jaddada hakan ,tare da cewar da shi da ministocin sa, za su ƙaurace taron na ƙasar Portugal, da zaran dai ya samu halartar shugaban Zimbabwe.

A martanin da ya maida, shugaban hukumar zartsarwa mna ƙungiyar taraya turai, ya ce ba ta kamata ba, a maida Zimbawe saniyar ware a wannan taro, domin haɗuwa ce da ta ƙunshi dukan ƙasashen Afrika da na ƙungiyar EU.

Ɗaukar irin wannan mataki, ba zai taimaka ba, wajen kawo ƙarshen rikicin da ke wakana a Zimbabwe.