1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Human Rights Watch ta zargi Burma da tilasatawa yara aikin soja

October 31, 2007
https://p.dw.com/p/C15K

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights watch tace sojojin kasar Burma suna tilasatawa yara aikin soja akasar.Wani rahoto da kungiyar wadda ke da zama a birnin Newyork ta fitar yace yara yan akalla shekaru 10 ne ake lakadawa duka ko kuma ake barazanar tsare su a kokarin tilasata masu shiga aikin soaj a kasar ta Burma.Rahoton yace rundunar sojin Burma tana tilasatawa wadannan yara ne saboda bukatun kara habaka rundunar,sakamakon janyewa da ake yi daga aikin soja da kuma cewa manya basa son shiga aikin na soja.Rahoton yayi kira ga komitin sulhu na MDD daya kafa takunkumi da zai hada da na makamai kann gwamnatin mulkin soja na Burma.