Hulɗa tsakanin Jamus da Turkiya | Labarai | DW | 30.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hulɗa tsakanin Jamus da Turkiya

Ƙasashen Jamus da Turkiya za su ƙarfafa hulɗar musayar al'adu da ta kasuwanci domin amfanin ƙasashen biyu

default

Merkel da Erdogan

A rana ta biyu ta ziyar da ta kai ƙasar Turkiya, shugabar gwamnatin Jamus Agela Merkel, ta ziyarci cibiyoyin al'adu da kasuwanci a ƙasar. Merkel ta kuma jaddada buƙatar inganta hulɗar musayar al'adu tsakanin ƙasashen biyu. Ta bayyana hakane ya yin  da ta ziyarci wata makarantar jamusanci dake birnin Instanbul. Ƙasashen biyu yanzu haka suna yunƙurin kafa wata jami'ar haɗin gwiwa tsakaninsu, wanda za a kafa cikin ƙasar ta Turkiya. Yanzu haka abinda ake jira domin kafa wannan jami'ar shine amincewa majalisar dokokin Turkiya, abinda Merkel ta nuna fatar samun amincewa. Tun farko dai shugabar gwamnatin Jamus ta tattauna da Firimiyan ƙasar Tayyip Erdogan, inda suka taɓo batun shigar da Turkiya cikin Tarayyar Turai da kuma abinda ya shafi kafa makarantun harsunan Turkiya anan Jamus. Izuwa yanzu shugabar gwamnatin Jamus, ta ci gaba da nuna matsayin ta na yin adawa da shigar da Turkiya cikin EU, sai dai ta kasance abokiya ta musamman. 'Yan ƙasar Turkiya dai su suka fi ko wace ƙasa yawa a ƙasar Jamus

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi