1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin Radi a ƙasar Afghanistan

March 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4J

Gwamnatin Jamus ta yi kira ga ƙasar Afghanistan ta yi sassauci ga wani ɗan ƙasar Afghanistan Abdul Rahman wanda ke fuskantar hukuncin kisa a sakamakon yin Rida. Abdul Rahman wanda ya shafe shekaru tara yana zaune a ƙasar Jamus, ya yi rida inda ya bar addinin musulunci ya koma ga addinin Kirista. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya shaidawa jaridar Frankfurter Rundchau cewa gwamnatin Jamus ta nemi gwamnatin Afghanistan ta martaba yancin addini ga kowane dan Adam. Steinmeier, yace yancin barin kowane mahaluki ya yi addinin sa, na kunshe a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar Afghanistan da kuma ƙudirin kare haƙƙin bil Adama na ƙasa da ƙasa wanda Afghanistan ta sanya hannu a kai. ƙasar Jamus na da dakarun soji 2,400 a Afghanistan waɗanda ke aikin kiyaye zaman lafiya a karkashin ƙungiyar tsaro ta NATO.