Hukuncin laifukan yaƙi a Yugoslaviya. | Labarai | DW | 10.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin laifukan yaƙi a Yugoslaviya.

A yanke hukuncin ɗauri ga masu laifukan yaƙi a Serbiya.

default

Zaman kotun MƊD akan laifukan yaƙin Yugoslaviya.

Kotun da Majalisar Ɗinkin Duniya(MDD) ta kafa domin hukunta laifukan yaƙi da aka aikata a Yugoslaviya ta samu wasu manyan sojoji, Serbiyawan Bosniya guda biyu, da laifin aiwatar da kisa akan muslimin Serbiya sama da dubu bakwai a garin Srebrenica a shekara ta 1995. Kotun da ke da mazauninta a birnin the Hague na ƙasar Holland ta yanke hukunci ɗaurin rai da rai akan Vujadin Popovic da Lyubisa Beara. An kuma  yanke ma wani hafsin soji, hukuncin ɗauri na shekaru 35  a gidan kaso bisa laifin ba da taimako wajen yin kisa ga musulmin na Serbiya, a baya ga wasu mutane huɗu da aka yanke wa hukunci ɗauri na shekaru biyar zuwa sha tara bisa aikata laifukan yaƙi.

Mawalafiya. Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal