1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin laifukan yaƙi a Yugoslaviya.

June 10, 2010

A yanke hukuncin ɗauri ga masu laifukan yaƙi a Serbiya.

https://p.dw.com/p/Nno0
Zaman kotun MƊD akan laifukan yaƙin Yugoslaviya.Hoto: dpa

Kotun da Majalisar Ɗinkin Duniya(MDD) ta kafa domin hukunta laifukan yaƙi da aka aikata a Yugoslaviya ta samu wasu manyan sojoji, Serbiyawan Bosniya guda biyu, da laifin aiwatar da kisa akan muslimin Serbiya sama da dubu bakwai a garin Srebrenica a shekara ta 1995. Kotun da ke da mazauninta a birnin the Hague na ƙasar Holland ta yanke hukunci ɗaurin rai da rai akan Vujadin Popovic da Lyubisa Beara. An kuma  yanke ma wani hafsin soji, hukuncin ɗauri na shekaru 35  a gidan kaso bisa laifin ba da taimako wajen yin kisa ga musulmin na Serbiya, a baya ga wasu mutane huɗu da aka yanke wa hukunci ɗauri na shekaru biyar zuwa sha tara bisa aikata laifukan yaƙi.

Mawalafiya. Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal