Hukuncin Kotun Koli Ta Jamus | Siyasa | DW | 24.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukuncin Kotun Koli Ta Jamus

Kotun kula da daftarin tsarin mulkin Jamus ta ce ana iya kwace takardun wani dan Nijeriya da yayi karya domin zaman dan Jamus

Shugaban Kotun Koli ta Jamus

Shugaban Kotun Koli ta Jamus

Kara da dan Nijeriyar Benjamin O ya daukaka dangane da kwace takardunsa na dan kasar Jamus bai cimma nasara ba. Domin kuwa bisa ga ra’ayin alkalai a kotun koli mai kula da daftarin tsarin mulkin kasar duk wanda ya gabatar da bayanai na karya domin neman takardun zama dan kasa ba zai iya sake dawowa yayi hujja da kudurin daftarin tsarin mulkin ba. Shi dai dan Nijeriyar, a lokacin da ya gabatar da takardunsa na neman zama dan kasar Jamus yayi ikirarin cewar wai yana da aiki kuma a saboda haka yana da ikon ciyar da iyalinsa, alhali kuwa ba ya da aikin yi, kuma a hakika yana fatauci ne da hodar ibilis. A sakamakon haka karamar hukumar Pforzheim ta kwace takardun nasa a shekara ta 2002. Alkalan kotun kolin suka ce karamar hukumar na da ikon yin haka, kamar yadda aka ji daga bakin Winfried Hassemer, shugaban kotun:

“Duk wanda yayi amfani da wata hanyar da ba ta dace ba, Ya-Allah mataki ne na yaudara ko rashawa ko ci da ceto domin neman zama dan kasa ba zata yiwu a yi marahabin lale da shi daidai da wanda ya bi sahihiyar hanya ta gaskiya domin cimma burinsa ba.”

Wannan mataki zai iya zama gargadi ga sauran mutanen da watakila suke da shirin gabatar da bayanai na karya domin neman takardun zama ‘yan kasar Jamus nan gaba. Shi dai Benjami O. Da gangan ya gabatar da wadannan bayanai na kage kuma tilas ne ya hakura da kaddarar da ta rutsa da shi yanzun na cewar ba ya da kasa. Kuma kakkabe shi daga wannan hakki na zama dan kasar Jamus da aka yi ya dace da tsarin dokoki na kasa da kasa.

Shi dai lauyan dake kare dan usulin Nijeriyar ya nuna rashin gamsuwarsa da hukuncin da kotun kolin ta yanke, ko da yake ba za a kore shi kai tsaye daga harabar Jamus ba, saboda yana auren Bajamushiya. Lauyan nasa ya kara da cewar:

“Ko da yake ba za a kore shi ba saboda yana auren Bajamushiya, amma matsalar dake akwai shi ne a game da izinin aiki, wanda aka hana masa, kuma ga alamu da wuya samu nan gaba. Wannan shi ne kawai abin da zamu mayar da hankali kansa wajen ganin lalle ya samu izinin kama aiki a nan kasar.”