1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisan kiyashin Ruwanda

June 11, 2010

Kotun Finnland ta yanke hukunci akan kisan kiyashin Ruwanda.

https://p.dw.com/p/Nouf
Emmanuel Murangira, ɗaya daga cikin 'yan ƙabilar Tutsi da suka tsira da rayukansu a shekarar 1994.Hoto: AP

Wata kotu ta ƙasar Finnland ta yanke ma wani tsohon limamin coci na ƙasar Ruwanda hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari. Kotun ta samu Fracois Bazaramba da laifin hannu a kisan kiyashin da ya auku a ƙasar ta haifuwarsa a shekarar 1994. A cikin shar'iar, kotun ta ce matakin da tsohon limamin cocin ya ɗauka ya bayyanar da aniyarsa ta gusar da wani yanki ko kuma baki ɗayan 'yan ƙabilar Tutsi daga doron duniya. Gidan telebijan Finnland ya ba da rahoton da ke nuni da cewa Bazaramba ya yi shirin ɗaukaka ƙara akan hukuncin da aka yanke masa. A watan Afrilun shekara ta 2007 ne dai 'yan sandan ƙasar Finnland suka cafke shi bisa zargin da aka yi masa na taka rawa a kisan kiyashi da aka yi wa mutane kimanin dubu 800.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu