Hukuncin kason rai da rai ga Carlos | Labarai | DW | 28.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin kason rai da rai ga Carlos

Wata kotun kasar Faransa ta yanke hukuncin kason na rai da rai ga Ramirez Sanchez da aka fi sani da Carlos mashahurin dan ta'adda dan kasar Venuzuwela da ya yi kaurin suna a shekarun 1970 zuwa da 1980. 

 

Kotun ta yanke masa wannan hukunci ne bayan da ta same shi da laifin kai wani harin ta'addanci a birnin Paris a shekarar 1974, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu 34. Sau biyu dama a baya kotun kasar ta Faransa wacce ke tsare da Carlos din dan shekaru 67 ta yanke masa hukuncin zaman wakafi na sai illa masha Allahu. 

Sai dai lauyoyin Ramires Sanchez din sun bayyana aniyarsu ta daukaka kara a kan wannan hukunci wanda suka ce ba yi adalci a cikinsa ba.