Hukuncin haɗarin kamfanin Union Carbide. | Labarai | DW | 07.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin haɗarin kamfanin Union Carbide.

Kotu a Indiya ta yanke hukunci ɗaurin shekaru biyu gami da tara ga masu hannu a haɗarin kamfanin Union Carbide mai haɗa sinadaran kimiyya a birnin Bhopal.

default

Kamfani Union Cabride mai haɗa sinadarin kimiyya na Bhopal a Indiya

Wata kotu a ƙasar Indiya, ta yanke hukunci akan ta´asar da ta wakana yau shekaru 25 da suka gabata, a kamfanin gas na Union Carbide mallakar Amurika dake birin Bhopal na Indiya.

Ranar ukku ga watan Desemba na shekarar  1984 wasu tankokin gas suka farfashe a wannan kamfani, wanda suka yi sanadiyar mutuwar dubunan mutane.

Kotu tace wasu jami´an bakwai na kamfanin sun nuna sakaci, saboda haka  ta yanke masu hukunci ɗaurin shekaru biyu tare da biyan tara ta Euro 1.800.

To sai dai wanda suka ƙetara rijiya da baya cikin wannan bila´i, da kuma Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani Adama, sun yi watsi da wannan hukunci wanda suka danganta da tsabar rashin adalci, saboda haka sun ɗaura ɗamara ci gaba da gwaggwarmaya, har sai an tabbatar da hukunci  na gaskiya.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Abdullahi Tanko Bala