Hukunci kotu a kan mataimakin Shugaban Iraqi | Labarai | DW | 12.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukunci kotu a kan mataimakin Shugaban Iraqi

Babbar kotun Iraqi ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar Iraqi Taha Yasin Ramadan.

Alkalin Kotun Ali al-Kahachi wanda ya yanke hukuncin yace ya kamata mataimakin shugaban kasar ya bi sahun Saddam Hussain ta hanyar rataya bisa samun sa da hannu a kisan mutane 148 yan shiá daga garin Dujail a tsakanin shekarun 1980. Kotun ta yanke masa hukuncin kisa duk kuwa da roko daga jamián majalisar ɗinkin duniya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu fafutukar kare haƙƙin bil Adama. Da yake jawabi kafin yanke masa hukuncin tsohon mataimakin shugaban ƙasar Taha Yasin Ramadan yace Allah ya sani bai aikata komai ba.