Hukunci kan Marc Ravalomanana
August 28, 2010Wata kotu a ƙasar Madagaska, ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Marc Ravalomanan hukuncin ɗaurin rai da rai, da yin aiki mai tsanani. An samu Ravalomanana da laifin kisan kai da bada umarnin yin kisan kai, a lokacin murƙushe masu zanga zangar adawa da gwamnatinsa a bara. An yankewa tsohon shugaban hukunci ne a bayan idonsa. A barane dai masu tsaron tsohon shugaban suka buɗe wuta ba tare da gargaɗi ba kan masu zangaga, inda aka hallaka mutane 30 wasu kimanin ɗari suka jikkata. Wannan zanga zangar dai taci gaba abinda kuma yakai ga hamɓarar da gwamnatin Ravalomanan, kuma tun lokacin yake mafaka a ƙasar Afirka ta kudu. Hukuncin wani ko ba yane ga yunƙurin ƙungiyar Tarayyar Afirka dake fafitakar a warwaren matsalar siyasar Madagaska.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita. Abdullahi Tanko Bala