1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci akan tsohon ministan Afrika ta kudu

Zainab MohammedAugust 17, 2007

Mulkin wariyar launin fata ya shige

https://p.dw.com/p/BvSl
Adriaan Vlok
Adriaan VlokHoto: AP

Wata babbar kotun kasar Afrika ta kudu ta ta zartar da hukuncin daurin shekaru 10 akan wani tsohon ministan kasar zamanin mulkin nuna wariyar launin fata da wasu jamian yansanda guda 4,kana aka ragwanta hukuncin zuwa shekaru 5,saboda amincewa da laifin yunkurin kisan gilla wa wani bakin fata a shekarata 1989.

An zartar da wannan hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kurkuku ne Tsohon minista Andrian Vlok da tsohon babban jamiin rundunar yansanda Johann van Der Merwe,hukuncin da aka rageshi zuwa shekaru biyar,a wannan sharia dake zama wani sabon babi na harkokin shariar wannan kasa dake cigaba da kasancewa da tarihin irin illoli da turawa sukayi lokacin mulkinsu.

Wanda ake zargin dai yayi kokarin aiwatar da kisan gilla ne akan wani bakin fata mai fafutukar nemarwa bakaken fatu yan uwansa yanci a wancan lokaci,kuma babban limamin churchi Frank Chikane,wanda yanzu ke zama mai bawa shugaba Thabo Mbeki shawarwari.An yi kokarin kashe wannan jamiin ne ta hanyar sanya masa guba a kayayyakin jikinsa,gubar data janyo masa jinya na tsawon lokaci saboda irin illa datayiwa lafiyarsa.

Mai shekaru 70 da haihuwa Adriaan Vlok ya bayyana gamsuwarsa da wannan hukunci dacewa

“Yace godiya nake dangane da fahintarku,da goyon bayan da kuka bamu,kuma idan muka duba halin da kasarmu take ciki ayau,sai ince don Allah kowa yabi doka ya kuma daraja mata don ta hakan ne zamu kai kasarmu ga daukaka”

Ma gabatar da karar Anton Ackermann yace wannan sharia wadda tazo shekaru 13 bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata da ake kira Apatheid,ba yana bayyana ramuwar gayya bace,wanda irin hukuncin nasu ke bayyanawa,musamman bayan da Mr Vlok da sauran masu laifin sun amince da laifin da ake zarginsu dashi,kuma suka bukaci da ayi musu rangwame.

A wajen kotun Pretorian dai daruruwan mutane sunyi cincirundo dauke da kwalaye dauke da rubuce rubucen dake Allah wadan zamanin nuna wariyar launin fata,wanda ya sabawa biladama.Inda suka nemi da ayi adalci tare da tabbatar da hukunta wadannan mutane da suka tozartawa bakaken fatan kasar ta Afrika ta kudu a baya,kamar yadda mai magana da yawun wata kungiya da ake kira Afriforum Kallie Kriel ya bayyana…..

“Yace kawo yanzu baa taba gurfanar da jamii guda daga jammiiyyar ANC ba saboda take hakkiin biladama,duk dacewa kimanin tsoffin shugabannin jammiiyyar 37 ne suka gabatar da kansu gaban hukumar.Abunda muke buketa shine a dauke matakai na gurfanar da masu laifi tare da zartar da hukuncin daya dace akansu,saboda irin cin zarafin mutane da suayi a Baya..”