1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukunci ɗaurin rai da rai ga tsofan shugaban ƙasar Phillipnes Joseph Estrada

Wata kotu a Manille baban birnin ƙasar Phillipine, ta yanke hukunci ɗaurin rai da rai, ga tsofan shugaban ƙasa Joseph Estrada, wanda aka tuzhuma da sama da fadi da dukiyar jama´a.

A cewar kotun da ke kulla da shari´a cin hanci da rashawa, Estrada dan shekaru 70 a dunia, ya sace a ƙalla dalla milion 87,a tsawan shekaru 2 da rabi da yai na jagorancin ƙasar Philipines.

A halin yanzu ,wannan magudan kuɗaɗe na jibge cikin bakunan ƙasashen ƙetare, saidai bai da izinin ɗaukar sisin kwabo, a sakamakon takunkumin da aka ƙargama masu.

Kotun ta buƙaci bankunan su maida wannan kuɗin haram, ga assusun gwamnatin Philipines.

A shekara ta 2001 ne, jama´ar ƙasar Philipines ta tada bori, wanda ya kiffar da shugaba Joesph Estrada.

Mataimakiyar sa, Gloriya Arroyo ta maye gurbin sa kimanin watani 6 da su ka wuce, ta ƙaddamar da wani gagaramin shiri, na yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa.