Hukumomin Tchad sun ƙi amincewa da karɓar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a iyakar su da Sudan | Labarai | DW | 01.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Tchad sun ƙi amincewa da karɓar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a iyakar su da Sudan

Hukumomin ƙasar Tchad, sun bayyana adawa ga rundunar kwantar da tarzoma da Majalisar Ɗinkin Dunia ke bukatar aikawa, a iyakar Tchad, da yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Sanarwar da fadar mulkin NDjamena ta hiddo, ta nunar da cewa, a maimakon rundunar sojoji, Tchad na iya amincewa da tawagar yan sanda, domin su kulla da tsaron yan gudun hijira.

Sanarwar ta zo kwastam! ga jami´an diplomatia, domin shugaba Idriss Deby da kan sa, ya bayana amincewa da karɓar rundunar ta Majalisar Dinkin Dunia, albarkacin ziyara aikin da Praministan Ministan France, Dominique de Vilepin ya kai Tchad, a watan november, na shekara ta 2006.

A watan Februaru da ya gabata, Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, tunni, har ya yanke shawara aika dakaru dubu 6, zuwa dubu 10, a iyakokin ƙasashen Tchad, da Jamhuriya Afrika ta tsakiya, da kuma Sudan, da zumar hana yaɗuwar matsalolin yankin Darfur .