1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Sudan sun jaddada matsayin su na watsi da dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur

June 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuuP

Hukumomin ƙasar Sudan, sun jaddada matsayin su, na ƙin amincewa, da karɓar dakarun kwanta da tarzoma na Majalisar Ɗinkin Dunia, a yankin Darfur.

Mashawarcin ƙut da ƙut na shugaban ƙasa Omar El Beshir ya bayyana wannan sanarwa a yammacin jiya.

Majzub al- Khalifa Ahmed, ya mussanta batun maye gurbin dakarun kwantar da tarzoma na ƙungiyar Taraya Afrika, da na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Ya ce yarjenejiyar da a ka rattaba hannu kanta, a birnin Abuja, tsakanin yan tawayen Darfur, da gwamnati ba ta ƙunshi matakin aika dakaru ba, daga Majalisar Ɗinkin Dunia.

A Ƙarshen shekara da mu ke ciki ne, komitin sulhu ke shirye shiryen, tura rundunar sojoji a yankin, bisa gayatar Ƙungiyar Taraya Afrika.

A cikin bayanin da ya yi kakakin shugaban El Beshir, ya bukaci kaɗai, Ƙungiyar AU, ta ƙarffafa dakararun ta a yankin.