Hukumomin leken asirin Syria da Lebanon na da masaniya akan kisan Hariri
October 21, 2005Talla
Wani binciken da MDD ta yi ya nuna cewa manyan jami´an leken asirin kasashen Syria da Lebanon na da hannu a kisan gillan da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. Kamar yadda rahoton wanda mai shari´a Detlev Mehlis na nan Jamus ya nunar, kisan na Hariri a ranar 14 ga watan fabrairu na da daure kai ta yadda da wuya a iya gane cewar hukumomin leken asirin Syria da Lebanon ba su da wata masaniya dangane da kisan. Rahoton mai shafuka 53 ya bayana cewar har yanzu ba´a kammala binciken ba kuma dole za´a ci-gaba da wannan bincike tare da hadin kan hukumomin shari´a da na tsaron Lebanon. A jiya an girke sojoji da ´yan sanda kimanin dubu 10 a fadin kasar ta Lebanon a wani mataki da jami´ai suka bayyana da cewa dokar ta baci a fakaice.