Hukumomin Lebanon sun kame wani da ke shirin kaiwa Jamus hari | Labarai | DW | 13.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Lebanon sun kame wani da ke shirin kaiwa Jamus hari

Gwamnatin Jamus ta ce hukumomin Lebanon sun faɗa mata cewar sun yi amana wasu masu tsauttsauran ra´ayin na shirin ƙaddamar da hare-haren ta´addanci a cikin Jamus. Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a ma´aikatar shari´a wadda aka bayyana da cewa za a kaiwa harin. Wannan gargaɗi ya fito fili ne bayan da aka kame wani da ake zargin cewa ɗan al-Qaida ne a birnin Beirut. Rahotannin sun yi nuni da cewa a farkon wannan makon mutumin ya buga waya zuwa ofishin jakadancin Jamus dake Beirur inda ya yi barazanar kai hare-haren akan ma´aikatun gwamnatin Jamus a matsayin daukar fansa ga hukuncin ga shari´ar da ake yiwa wasu ´yan al-Qaida a nan Jamus.