Hukumomin Jamus sun kame wani mutum da ake zargi da shirin dana bam cikin jirgin kasa | Labarai | DW | 19.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Jamus sun kame wani mutum da ake zargi da shirin dana bam cikin jirgin kasa

Masu shigar da kara na tarayyar Jamus sun ce hukumomin kasar sun kama mutum daya da ake zargi da hannu a shirin dana bama-bamai cikin wasu jiragen kasa a karshen watan jiya. Suka ce sun yi imani mutumin na daya daga cikin wasu mutane biyu da wata kyamara da aka kafa a tashar jirgin kasa ta birnin Kolon ta dauki hotonsu a ranar 31 ga watan yuli. An kama mutumin ne da sanyin safiyar yau asabar a babbar tashar jiragen kasa ta birnin Kiel dake arewacin Jamus. Masu bincike sun yi zargin cewa an bar bama-baman a tashoshin jiragen kasa na biranen Dortmund da Koblenz da nufin kai harin ta´addanci a cikin kasar.