Hukumomin Ingila sun bankado wani shirin sanya bama bamai a jiragen sama | Labarai | DW | 10.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Ingila sun bankado wani shirin sanya bama bamai a jiragen sama

Hukumomi a Ingila a yau sun sanar da cewa sun dakatar da wani shiri da ´yan tarzoma suka yi na sanya bama-bamai, domin rushe jiragen sama masu yawa a lokaci guda, kan hanya daga London zuwa Amirka. ´Yan sanda sun yi bayanin cewar sun dakatar da abin da suka kira, wani shiri na kisan kare-dangi da ´yan tarzoman suka yi. Yanzu haka dai dimbin matafiya ne suka yi cincirindo a wuraren bincike da aka kakkafa, yayin da jami´an tsaro suke binciken kayayyakin da fasinjojin zasu shiga jiragen saman da su. Yanzu haka dai an rufe babbar tashar jiragen sama ta Heathrow dake birnin London, yayin da Amirka ta kara tsananta matakan tsaro a bangaren zirga-zirgar jiragen saman fasinjoji na kasar. Ya zuwa yanzu an kama mutane ashirin da daya da ake zargin su da kokarin sanya bama-bamai cikin jiragen saman na Ingila.